Mintuna 30 da suka wuce Lokacin karatu: Minti 3 A yayin da aka shiga watan Sha’aban, wanda daga shi sai Ramadana, mai tsarki da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Musulunci, al’ummar Musulmin na shirye-shiryen zuwan watan, wanda a cikinsa ake kara azama wurin ibada. Daga cikin shirye-shiryen da ake yi akwai ramakon bashin azumi na watan Ramadan na bara, ga waɗanda suka sha